Friday, 25 October 2013

(in hausa) jumma’a, oktoba 25 RHAPSODY OF REALITIES

Sunansa Mai Ba Al’ajibi · jumma’a, oktoba 25

PASTOR CHRIS

Sai Yesu ya matso, ya ce musu, an mallaka mini dukkan iko a sama da kasa. Don haka sai kuje ku almajirtar da dukkan al’ummai, kuna yi musu baftisma da sunan uba, da na Da, da na Ruhu Mai Tsarki, kuna koya musu su kiyaye duka abin da na umurce ku... (Matiyu 28:18-20).
Pastor Chris In an suke haifuwanka, an sa maka sunan yesu kenan wannan suna shine suna mafi girma da aka bayyana ga mutum, don ta wurin sunan ne Allah ya hallici komai. Allah ya bada dukkan iko ga wannan suna mai al’ajibi Yesu Kristi.
Kalma ta fada mana cewa yesu ya bamu ikonsa, ya kuma umurce mu, mu almajirtar da al’ummai, da sunansa ya ce, "...Kuna yi musu baftisma da sunan uba, da na Da, da na Ruhu Mai Tsarki." Almajirai sun ba umurnin Yesu, suka kuma yi baftisma da sunan Yesu (Ayyukan Manzanni 2:38, 8:16, 10:48, 19:5, 22:16). Sun gane da maganan Yesu. Sun san cewa, sunan nan Yesu shine sunan uba na sama. In kace "cikin sunan yesu" kana nufin sunan Allah ubangiji kenan.
Kolosiyawa 1:19 tace "A gareshi dukkan cikar Allah ta tabbata, domin Allah yana farin ciki da haka." Cikar Allah na sama yana zaune cikin yesu – sunanda ya fi gaban dukan sunaye. Ka yi fariya da sunan yesu. Filibiyawa 2:10 ta ce, "...domin kowace gwiwa sai ta rusuna wa sunan nan na yesu, a sama da kasa, da kuma can Karkashin kasa." Kome da kowa da ke a sama, kasa, suna karkashin yesu ne.
Furtawa
Ya uba, na gode don ka bani iko in yi amfani da sunan yesu. Ina rayuwa da ikon sunan nan yau, cikin nasara da adalci. Ina da salama, cingaba, karuwa, nasara da wadata kullum, cikin sunan Yesu. Amin.
ka r i n bincike :Luka 10:19; Filibiyawa 2:9-11

AYAR KOWACCE RANA

Shirin Shekara na Karatun Bible : Ishaya 64-66 2 Timothawus 1:1-18
hirin shekara 2 na karanta Bible : Yahaya 7:32-44 2 Sarakuna 13-14

No comments:

Post a Comment